Nadal ya tsallake Murray

rafeal nadal
Image caption Nadal ya yi watanni bakwai yana jiyyar ciwon guiwa bayan gasar Wimbledon ta bara

Rafeal Nadal zai je gasar tennis ta Amurka a matsayin na biyu a jerin gwanayen wasan a duniya bayan da ya yi nasarar gasar Cincinnati.

Nadal ya zarta mai kare kambun gasar ta Amurka ne Murray wanda za a bayyana a matsayin na uku a duniya a lokacin gasar da za a fara a New York ranar 26 ga watan Agusta.

Nadal dan Spaniya ya buge John Isner ya dauki kofinsa na tara a 2013 a Cincinnati.

A da ya samu koma-baya ya zuwa matsayi na biyar a duniya amma yanzu ya dawo na biyu a karon farko tun watan Yuli na 2012.

Tun lokacin da ya warke a watan Fabrairu daga raunin da yai fama da shi Nadal ya je wasan karshe sau 11 a gasanni 12 da ya shiga.

Ya yi nasara a guda tara inda Steve Darcis ya fitar da shi a zagayen farko a gasar Wimbledon.

Yanzu zai tunkari gasar ta Amurka ne (US Open) a harin da yake na daukar kofin a karo na biyu, kuma ya ci gaba zuwa karshen shekarar da burin zama na daya.

Roger Federer kuwa ya yo kasa n da mataki biyu daga na biyar a duniya.

Karin bayani