Najeriya ta gamu da cikas a wasan Kofin Duniya

aminu maigari
Image caption NFF da kociyan 'yan wasan sun ce suna kokarin ganin wadanda suka cancanta kawai aka dauka

Najeriya za ta je wasan gasar Kofin Duniya na 'yan kasa da shekaru 17 a watan Oktoba ba tare da gwanayen 'yan wasanta ba.

Fitattun 'yan wasan da aka yi musu gwajin shekaru an gano cewa sun wuce shekaru goma sha bakwai na ka'idar shiga gasar.

Tawagar wadda ta zo ta biyu a gasar ta 2013 ta Afrika a Morocco an yi wa 'yan wasan nata gwajin ne a Abuja domin tantance gaskiyar shekarun nasu kafin tafiya gasar ta duniya a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Duk da wannan koma-baya da tawagar ta samu mai horad da 'yan wasan Manu Garba ya jaddada cewa zai iya samar da tawaga mai karfi kafin watan na Oktoba.

Sau uku Najeriya ta dauki Kofin na Duniya na 'yan kasa da shekaru 17, a 1985 da 1993 da 2007 amma 'yan kallo da kafafen yada labarai na shakkun gaskiyar shekarun 'yan wasan kasar.

Zakarun Afrika na 'yan kasa da shekaru 17 Ivory Coast da Najeriya ta biyu da Tunisia da kuma Morocco sun yi nasarar zuwa gasar ta Duniya da za a yi daga 17 ga watan Oktoba zuwa 8 ga Nuwamba.

Karin bayani