Zabaleta ya sabunta kwantiragi

pablo zabaleta
Image caption Zabaleta ya ce,''shekara biyar na yi a nan kuma ina ji na kamar ina gida''

Dan wasan Manchester City na baya Pablo Zabaleta ya sanya hannu a kwantiragin kara shekaru hudu a kungiyar.

Mai sheakaru 28 wanda aka zaba gwarzon dan wasan kungiyar a bara zai kammala kwantiraginsa yanzu a shekara ta 2017 a City.

Zabaleta dan Argentina ya yi wa kasarsa wasa sau 31 kuma ya rike mukamin kyaftin a Man City tsakanin watan Janairu da Maris na bara lokacin da Vincent Kompany ya ji rauni.

Ya buga wa kungiyar wasanni sau 22 a kakar wasanni ta 2011-12 lokacin da City ta dauki babban kofinta a karon farko cikin shekaru 44.

Kuma shi ne ya ci kwallon farko lokacin da suka ci Queens Parjk Rangers 3-2 a ranar karshe ta Premier.

Karin bayani