Yadda wasannin Europa suka kasance

shakhter ta casa celtic
Image caption Fatan Celtic na shiga gasar Europa matakin rukuni ya gamu da tangarda

An yi wasannin neman shiga matakin rukuni rukuni na gasar Kofin Europa na kwallon kafa guda biyar a Talatar nan.

Shakhter Karagandy ta Kazakhstan a gida ta lallasa Celtic ta scotland da ci 2-0.

Viktoria Plzeň ta Czech ta casa bakinta 'yan Maribor ta Slovenia 3-1, Olympique Lyonnais ta Faransa a gidanta ta gamu da rashin sa'a da ci 2-0 a hannun Real Sociedad ta Spaniya.

Paços de Ferreira ta Portugal ba ta ji da dadi ba a hannun Zenit ta Rasha da ta ziyarce ta da ci 4-1.

PSV ta Netherlands da AC Milan ta ziyarce ta sun tashi kunnen doki 1-1.

Duk bakuwar kungiyar da ta sanya kwallo daya a ragar mai masaukinta tana da maki biyu ne a maimakon daya bisa ka'ida.

A ranar Laraba ta sama za a yi karo na biyu na wasannin.