Evian ta sayar da Mohammed Rabiu

'yan wasan ghana
Image caption Krasnodar su ne na shida a wasan rukunin kasa da lig din Rasha da wasanni biyar

Kungiyar kwallon kafa ta Faransa Evian Thonon Gaillard ta amince ta sayar wa Kuban Krasnodar ta Rasha dan wasanta Mohammed Rabiu dan Ghana.

A bisa yarjejeniyar kungiyar ta Rasha za ta sayi dan wasan ne mai shekaru 23 akan fam miliyan 2.21 wanda ya yi wa Ghana wasa sau goma.

Rabiu da ke wasa a tsakiya ya buga wa Evian wasanni sau 64 tun suna rukuni na biyu har suka sami shiga gasar lig din Faransan ta Lig1, tun da ya koma daga Udinese a 2010.

A ranar Alhamis ne kungiyar ta Krasnodar za ta yi wasan neman shiga gasar Kofin Europa a gida karo na daya da Feyenoord ta Netherlands.

Karin bayani