Arsenal ta casa Fenerbahce

Aaron Ramsey ya ci wa Arsenal ta biyu
Image caption Kafin hutun rabin lokaci a ci kwallayen hankalin Arsenal ya tashi

Arsenal ta lallasa Fenerbahce ta Turkiyya a wasan neman shiga matakin rukuni rukuni na Zakarun Turai 3-0.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne a wasan da aka yi a gidan Fenerbahce a birnin Santambul aka ci kwallayen.

Kieran Gibbs ne ya fara ciwa Arsenal din bayan da Theo Walcott ya dauko wata kwallo ta gefe.

Aaron Ramsey ne kuma ya biyo baya da ta biyu, sannan kuma Olivier Giroud ya ci ta uku da bugun daga-kai-sai-maitsaron-gida.

A ranar Talata 28 ga watan Agusta za a yi karo na biyu a gidan Arsenal.

Ga yadda sauran wasannin suka kasance:

Dinamo Zagreb 0-2 Austria Wien: Ludogorets 2-4 Basel

Schalke 04 1-1 PAOK: Steaua Bucure┼čti 1-1 Legia Warszawa