Chelsea ta tsira daga Aston villa

chelsea da aston villa
Image caption Duk da cin da Chelsea ta fara yi musu da farko Aston Villa ba su karaya ba

Chelsea ta tsira a hannun Aston Villa inda ta yi nasara a kanta da ci 2-1 a gasar Premier.

Kungiyar ta shiga gaba ne a minti bakwai da fara wasan bayan da Antonio Luna ya ci kansu da kwallon da Eden Hazard ya kwararo.

A na gab da tafiya hutun rabin lokaci ne kuma sai Christian Benteke ya fanshe kwallon a minti 45.

Chelsean ta ci kwallonta ta biyu ne bayan da Ivanovic ya zura kwallon da Lampard ya cillo a bugun tazara a minti na 73.

'yan wasan Aston Villa sun yi korafi kan kin korar Ivanovic da alkalin wasa ya yi bayan da ya bugi Benteke da guiwar hannu.

Haka kuma sun kara wani korafin kan alkalin wasa ya ki basu fanareti bayan da John Terry ya taba kwallon da hannu a mintunan karshe na wasan.

Yanzu Chelsea tana ta daya a tebur da maki shida a wasanni biyu, Aston Villa kuma ta biyar da maki 3 wasanni 2.

A wasanninta na gaba Chelsea za ta kara da manchester United da kuma Bayern Munich ta Jamus.

Karin bayani