Puncheon ya maye gurbin Zaha

jason puncheon
Image caption Southampton ta ce Puncheon ya tafi ne domin samun damar wasa akai-akai

Crystal Palace ta dauki aron dan wasan gefe na Southampton Jason Puncheon domin maye gurbin Wilfred Zaha.

Mai shekaru 27 Puncheon wanda ya koma Southampton daga Plymouth a 2010, sau 81 yana yi wa kungiyar wasa.

Kuma yana daga cikin fitattun 'yan wasanta na gasar Premier a bara.

A da ya yi wasa karkashin kociyan Crystal Palace Ian Holloway a Blackpool.

A watan Maris dan wasan ya sabunta kwantiraginsa da Southampton har zuwa shekara ta 2016.

Crystal Palace tana neman wanda zai maye gurbin Wilfred Zaha ne wanda ya koma Manchester United.

Karin bayani