Elmander ya koma Norwich

johan elmander
Image caption Elmander ya ce,'' ina matukar farin ciki wannan yarjejeniya ta tabbata.''

Dan wasan gaba na Sweden Johan Elmander ya koma Norwich City daga kungiyar Galatasaray ta Turkiyya.

Kungiyar ta sanar da komawar tsohon dan wasan Bolton di ne mai shekaru 32 a matsayin aro na shekara daya.

A lokacin da ya koma Bolton daga Toulouse ta Faransa a 2008 Elmander ya ci wa kungiyar kwallaye 18 a wasanni 92.

Dan wasan na Sweden ya bar Bolton din a karshen kwantiraginsa a 2011 ya koma Galatasaray.

Karin bayani