Keshi ya gayyaci 'yan wasa 18 na waje

  • 21 Agusta 2013
Image caption Tawagar Super Eagles

Mai horar da 'yan wasan Najeriya, Stephen Keshi ya bayyana 'yan wasa 18 dake buga kwallo a kasashen wajen da yake so su buga wa kasar wasa a karawarta da Malawi.

'Yan wasan cikin gida biyar ne za su hadu da wadancan 'yan wasa 18, domin taka leda a wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya da za a buga a Calabar, a watan gobe.

'Yan wasa kamar Nosa Igiebor da Emmanuel Eminike tun bayan cin kofin gasar nahiyar Afrika, a karon farko za su buga wa kasar wasa.

Keshi ya shaida wa BBC cewa "Ina farin cikin gayyatar wasu muhimman 'yan wasa a karon farko, tun bayan cin kofin gasar nahiyar Afrika."

Karin bayani