West Brom ta ba Anelka hutu

nicolas anelka
Image caption Anelka ya ce, ''Mutuwar Eric za ta bar babban gurbi a rayuwarmu''

West Bromwich ta ba wa dan wasanta Nicolas Anelka hutun sai abin da hali ya yi saboda mutuwar wakilinsa Eric Manasse.

Anelka wanda ya koma kungiyar a bana ya yi mata wasan farko ne ranar Asabar lokacin da suka yi rashin nasara 1-0 a hannun Southampton.

Mai shekaru 34 dan Faransan ba zai buga wasan da za su yi ba ranar Asabar da Everton kuma rahotanni na cewa yana shirin ritaya.

Anelka wanda ya yi kungiyoyi da dama inda ya yi wasanni 69 ya shiga kungiyarsa ta shida ke nan a Premier a kwantiragin shekara daya.

Ya dauki kofin Premier da Arsenal da Chelsea ya kuma yi wa kungiyoyin Liverpool da Manchester City da Bolton wasa.

Anelka ya kuma dauki Kofin Zakarun Turai da Real Madrid a 2000.

Karin bayani