Sunderland ta sayi Charis Mavrias

charis mavrias
Image caption Charis Mavrias shi ne na 11 da Sunderland ta saya a bana

Sunderland ta kammala sayen dan wasan Girka Charis Mavrias daga kungiyar Panathinaikos akan kudin da ba a bayyana ba.

Dan wasan mai shekaru 19 ya amince da kwantiragin shekaru uku a kungiyar da ake wa lakabi da Black Cats.

A 2010 ne Mavrias yana dan shekara 16 ya fara buga gasar Zakarun Turai inda ya zama dan wasa mafi karancin shekaru na biyu da ya shiga gasar.

Matashin ya buga wa Panathinaikos wasannin gida 59 na Turai 11 kuma ya ci kwallaye shida.

Ya buga wa kungiyar kasar Girka sau biyu, bayan kuma ya kasance a kungiyoyin kasar na 'yan kasa da shekara 17 da 19 da kuma 'yan kasa da shekara 21.

Charis Mavrias zai sanya wa Sunderland riga mai lamba 35.

Karin bayani