Chelsea ta jinkirta neman Rooney

wayne rooney
Image caption Mourinho ya ce Rooney shi ne dan wasan kawai da suke nema

Jose Mourinho ya ce kila Chelsea ta sake neman sayen Rooney a karo na uku amma kuma sai bayan karawarsu ta ranar Litinin da Man United.

Man United ta yi watsi da tayin da Chelsea ta yi na dan wasan mai shekara 27 sau biyu, tayi na biyun shi ne na fam miliyan 25.

Rooney wanda aka sa shi daga baya a wasan da Manchester United ta lallasa Swansea 4-1 na da niyyar barin kungiyar.

Duk da cewa kociyansu David Moyes ya kafe cewa ba za su sayar da shi ba.

A watan Yuli Mourinho ya ce Rooney ne dan wasan kadai da suke son saya.

Amma kuma kafin wasansu da Aston Villa ya ce akwai wadanda za su nema idan sun rasa tsohon dan wasan na Everton.

Karin bayani