Sharapova ta fice daga Gasar Amurka

maria sharapova
Image caption '' ba shakka daukar wannan mataki ba karamin abu ba ne akan daya daga cikin gasannin da na fi so''

Maria Sharapova ta fice daga gasar tennis ta Amurka da za a fara a sati mai zuwa saboda rauni a kafadarta.

'Yar kasar Rashan wadda ta dauki kofin gasar a 2006 ita ce ta uku a duniya a jerin gwanayen tennis da za su shiga gasar.

Amma yanzu Agnieszka Radwanska ta Poland ita ce ta zama ta uku.

Ta ce tun lokacin gasar Wimbledon ta ke kokarin magancin raunin amma abin ya ci tura.

Sharapova wadda ta dauki kofuna hudu na manyan gasanni na duniya ta ce a makwannin da ke tafe za ta mai da hankali wajen neman magani.

Karin bayani