Oboabona ya koma kwallo a Turkiya

Image caption Godfrey Oboabona

Godfrey Oboabona ya bayyana gamsuwarsa game da komawarsa taka leda a kungiyar Caykur Rizespor ta Turkiya bayan ya kulla yarjejeniya da ita.

Dan kwallon Najeriya ya bar Sunshine Stars ne ya koma Turkiya a kan Euro dubu 650.

Oboabona ya ce "wannan babban mataki ne kuma na zaku in soma taka musu leda"

Oboabona ya kulla yarjejeniyar shekaru hudu ne bayan an gwada lafiyarsa a kulob din a ranar Laraba.

Dan wasan mai shekaru ashirin da uku, ya kasance dan kwallon da ake yawan baiwa dama a Super Eagles tun lokacin da Stephen Keshi ya soma jan ragamar tawagar a shekara ta 2011.

Karin bayani