Tottenham ta ci Swansea

tottenham ta ci swansea
Image caption Tun ranar tara ga watan Disamba na 2012 wasanni biyu kawai aka ci Tottenham a Premier

Tottenham ta ci bakinta Swansea 1- 0 a wasansu na mako na biyu na gasar Premier.

Soldado ne ya ci kwallon da bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida a minti na 58

bayan da Jonjo Shelvey ya yi wa Andros Townsend keta.

Tottenham ita ce ta uku a tebur da wasanni biyu da kwallaye biyu da kuma maki shida

Swansea kuwa tana ta karshe wato ta 20 a wasanni biyu ana bin ta bashin kwallaye hudu

ba ta da maki ko daya.