Chelsea ta tabbatar da sayen Willian

willian borges da silva
Image caption Willian shi ne babban dan wasa na uku da Chelsea ta saya a bana

Chelsea ta tabbatar da sayen Willian dan Brazil daga Anzhi Makhachkala ta Rasha.

Amma kuma cinikin zai tabbata ne idan ya tsallake jarrabawar neman takardar izinin aiki.

Ranar Laraba ne zai fuskanci ganawar neman takardar izinin aikin a Birtania.

Dan wasan mai shekara 25 kiris ya kulla yarjejeniya da Tottenham amma Chelsea ta neme shi.

Ganin cewa zai buga gasar Zakarun Turai idan ya je Chelsea ake ganin hakan ya sa ya amince.

Ana ganin Chelsea ta saye shi ne akan kusan fam miliyan 30.

Wata majiya ta kusa da dan wasan ta ce tun 2011 Chelsea ke nemansa.

Willian ya fara buga wa babbar kungiyar kasar Brazil wasa da suka yi da Gabon

a watan Nuwamba na 2011.