Real Madrid ta yi nasara akan Granada

real madrid ta ci granada
Image caption Kwallon ita ce ta biyu da Karim Benzema wanda Arsenal ke nema ya ci wa Real Madrid

Real Madrid ta bi Granada har gida ta yi mata daya mai ban haushi.

Benzema ne ya ci kwallon minti goma da fara wasan na mako na biyu na gasar ta La Liga.

Yanzu Real Madrid ita ce ta biyar a tebur a wasanni biyu da kwallaye biyu a raga da kuma maki shida.

Ita kuwa Granada ita ce ta tara ba ta da kwallo a raga kuma tana da maki uku.

Barcelona ce ta daya a tebur din da kwallaye takwas da kuma maki shida.

Karin bayani