Man United da Chelsea sun yi canjaras

wayne rooney
Image caption Wayne Rooney da Chelsea ke nema ya buga wasan gaba daya

Manchester United ta tashi canjaras ba ci tsakaninta da Chelsea a Old Trafford.

Wasan shi ne na farko da David Moyes ya jagoranci United a gida tun da ya maye gurbin Sir Alex Ferguson.

Man United wadda wasanta na Premier na karshe da ta tashi ba ci tun a watan Mayu na 2009 ne da Arsenal ta fi zubar da damar jefa kwallo raga.

A Premier da ta wuce Chelsea ta yi nasara a Old Trafford 1-0.

Manchester United kuma ta yi galaba a Stamford Bridge 3-2.

Yanzu dai a karawarsu sau 43 a Premier sau hudu ke nan sun yi canjaras ba ci, a 1995 da 1988 da 2007 da kuma yanzu 2013.

United ta yi nasara sau 13 Chelsea kuma ta ci su sau 14.

Sannan kuma sun yi canjaras mai ci sau 15.

Karawar da suka yi da aka ci kwallaye da yawa ita ce ta 1954 Man United ta yi galaba da 6-5, a tsohuwar gasa ta rukuni na daya.