Moyes na tunanin haduwa da Chelsea

david moyes
Image caption Mourinho ya ce Moyes ne ya tunzara Rooney yake son barin Man United

Kociyan Manchester United David Moyes na tunanin kalubalen fuskantar Chelsea karkashin jagorancin Mourinho.

A wasansa na Premier na farko a gida a matsayin mai horar da 'yan wasan kungiyar.

Chelsea ta yi nasara a wasanninta biyu na farko kuma za ta baiwa Man United tazarar maki shida idan ta yi nasara.

Moyes ya ce ya yi wa tawagar 'yan wasansa abubuwa da dama kama daga zuwa rangadi da kuma wasa a Wembley.

To amma kuma haduwa da Chelsea a OldTrafford a wasan farko ba karamin abu ba ne.