Arsenal ta shiga gasar Zakarun Turai

Aaron Ramsey ya ci fenerbahce
Image caption Ramsey ya kara cin Fenerbahce a wasa na biyu

Arsenal ta samu nasarar shiga gasar Zakarun Turai a shekaru 16 a jere bayan da ta yi nasara akan Fenerbahce.

Kungiyar ta Turkiyya ta je gidan Arsenal ne da bashin kwallaye 3-0 na karawar farko ta neman shiga gasar.

A wannan wasan na biyu kuma Arsenal din ta kara musu kwallaye 2-0, jumulla sakamakon ya kasance 5-0.

Aaron Ramsey ne ya ci kwallayen ta farko a minti na 25 bayan hutun rabin lokaci a minti na 72 ya kara ta biyu.

Sai dai kuma dan wasan Arsenal din Lukas Podolski da alamu ya ji ciwo a cinyarsa.

Shima dan wasan Ingila Jack Wilshere ana ganin ya ji ciwo da aka buge shi a idon sawu.

Sakamakon Sauran wasannin Zakarun Turan:

Austria Wien 2-3 Dinamo Zagreb; Basel 2-0 Ludogorets

Legia Warszawa 2-2 Staeua Bucuresti;PAOK 2-3 Shalke04

Karin bayani