Malawi ta kai karar Keshi wajen FIFA

Saintfiet da Keshi
Image caption Saintfiet da Keshi

Hukumar kwallon kafa ta Malawi ta gabatar da korafi a gaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, game da kalaman mai horar da 'yan wasan Najeriya, Stephen Keshi.

Rahotanni sun ambato Keshi na bayyana mai horar da 'yan wasan Malawi, Tom Saintfiet da cewa ba dan Afrika bane, wani mai jajayen kunnnuwa ne, saboda haka ya koma Belgium.

Kalaman da Mr. Saintfiet ya dauke su a matsayin na nuna wariyar launin fata ne, hukumar ta FIFA dai ta tabbatar da karbar korafin.

An jima ana takaddama tsakanin Najeriya da Malawi game da zabar filin wasa na Calabar, domin buga wasan cancantar shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya.