Rooney ya sauya shawara

wayne rooney
Image caption Mourinho ya yi aniyar sayen wasu 'yan wasan idan Rooney ya ki zuwa Chelsea

Wayne Rooney ba shi da niyyar mika wa Manchester United bukatar barinsa ya sauya kungiya.

A ranar Litinin Mourinho ya ba wa dan wasan wa'adin sa'oi 48 ya bayyana matsayinsa ko yana son komawa Chelsea.

Sau biyu dai Chelsean ta gabatar da bukatar sayen dan wasan amma man United ta ce ba za ta sayar da shi ba.

Duk da ya bukaci barin kungiyar a da yanzu an sake dawo da shi ciki inda ya yi wasansu da Chelsea da suka tashi 0-0.

Har yanzu akwai wasu bukatunsa da suka shafi wasa a kungiyar da ba a warware ba duk da cewa ya fasa ficewa.

Karin bayani