Chelsea ta sayi Eto'o

Image caption Samuel Eto'o ya taka rawa sosai a kwallon duniya

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta sayi dan wasan gaba na kasar Kamaru, Samuel Eto'o, daga kungiyar Anzhi Makhachkala ta Rasha.

Dan wasan mai shekaru 32 a duniya ya koma kungiyar ne a yarjejeniyar shekara daya.

Kocin Chelsea, Jose Mourinho, ya nuna sha’awarsa ta sayen Eto'o bayan da sau biyu ana kin tayin da ya yi na sayen dan wasan Manchester United, Wayne Rooney.

A farkon makon da muke ciki, bayanai sun nuna cewa Rooney ba zai bar United ba, lamarin da ya sanya Chelsea suka hakura da batun sayensa.

Eto'o, wanda sau hudu yana zama zakaran kwallon kafar Afirka, yana daga muhimman ‘yan wasan da suka sanya kungiyar Inter Milan ta lashe gasar Champions a shekarar 2010.

Bayan nan ne kuma ya zama dan wasan da ya fi kowanne dan wasa tsada a duniya, lokacin da ya koma Anzhi a shekarar 2011.

Karin bayani