Dan Najeriya Nwafor ya koma Heerenveen

Image caption Uche Nwafor

Dan kwallon Najeriya Uche Nwofor ya koma kungiyar SC Heerenveen a matsayin aro daga VVV Venlo a Holland.

Dan shekaru 21, Nwofor ya nuna kin amincewarsa komawa taka leda a Rasha da kuma Turkiya.

Shi ne ya zira kwallaye biyun da Super Eagles ta doke Afrika ta Kudu da ci biyu da nema a wasan sada zumunci makwanni biyu da suka wuce a Durban.

Nwofor yace "Ina son in ci gaba da karatu na Holland kuma ina ganin wannan kulob din ne ya dace dani. Ina jiran soma kwallo a karkashin Marco Van Basten".

Karin bayani