Ban saba ka'ida ba kan Malawi - Keshi

Kocin Najeriya Stephen Keshi ya ce baiga wani abun da bai dace ba game da kalamansa a kan kocin Malawi Tom Saintfiet.

Hukumar kwallon Malawi ce ta kai Keshi kara zuwa Fifa bayan da ya kira Saintifet "farar fata ya koma Belgium".

Kalaman na Keshi a cewar hukumar kwallon Malawi kalamai ne na nuna wariyar launin fata, kuma sun biyo bayan bukatar kocin Malawi ne na an sauya filin wasa daga Calabar saboda batun tsaro.

Fifa ta tabbatarwa da BBC cewar ta samu takardar koke da wajen 'yan Malawi.

A ranar 7 ga watan Satumba ne za a fafata tsakanin Super Eagles da Malawi a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin Afrika da za a buga a Brazil.

Karin bayani