UEFA: Real za ta kara da Juventus

Image caption Yadda aka tantance kungiyoyin

Bayan da aka rarraba kungiyoyin kwallon kafa na Turai zuwa rukuni-rukuni a zagayen farko na gasar zakarun Turai, masana kwallon kafa na gannin cewar rukuni na biyu wanda ya kunshi Real Madrid da Juventus da Galatasaray da kuma FC Copenhagen ne rukunin da yafi zafi.

Mai rike da kofin wato Bayern Munich na rukuni na hudu tare da Manchester City da CSKA Moscow da kuma Viktoria Plzen.

Yadda aka rarraba kungiyoyin a rukuni-rukuni:

Rukunin A: Manchester United, Shakhtar Donetsk, Bayer Leverkusen, Real Sociedad

Rukunin B: Real Madrid, Juventus, Galatasaray, FC Copenhagen

Rukunin C: Benfica, Paris St-Germain, Olympiakos, Anderlecht

Rukunin D: Bayern Munich, CSKA Moscow, Manchester City, Viktoria Plzen

Rukunin E: Chelsea, Schalke, FC Basel, Steaua Bucharest

Rukunin F: Arsenal, Marseille, Borussia Dortmund, Napoli

Rukunin G: Porto, Atletico Madrid, Zenit St Petersburg, Austria Vienna

Rukunin H: Barcelona, AC Milan, Ajax, Celtic

Karin bayani