Sakamakon wasannin La Liga

messi da ronaldo
Image caption Messi da Ronaldo sun ci wa kungiyoyinsu kwallaye

Barcelona ta zama ta daya a gasar La Liga bayan da ta bi Valencia har gida ta yi mata 3-2.

Bayan ruwan kwallayen da aka yi a kashin farko na wasan inda aka ci dukkanin kwallayen biyar ba cin da aka yi bayan an dawo hutu.

Messi ne ya ci wa Barcelona kwallayenta uku yayin da Helder Postiga ya rama wa Valencia biyu.

Can kuma Atletico Madrid ta ci Real Sociedad 2-1 inda David Villa da Koke suka ci kwallaye biyun.

Espanyol ta yi canjaras ba ci tsakaninta da Real Betis yayin da Sevilla da Malaga suka yi 2-2.

Tun da farko Real Madrid ta ci Bilbao 3-1a wasan Cristiano Ronaldo ya ci daya Isco da kungiyar ta saya daga Malaga ya ci biyu.

Ibai Gomez shi ne ya jefa wa bakin kwallonsu daya