Liverpool ta yi nasara akan Man United

daniel sturridge
Image caption Daniel Sturridge ya ci Manchester United kwallonsa ta uku da take ba wa Liverpool nasara

Liverpool ta yi nasara mafi armashi ta fara gasar Premier tun kakar wasanni ta 1994-95 da ta ci Man United a Anfield.

Daniel Sturridge ne ya yi bikin cikarsa shekara 24 da haihuwa da kwallon da ya jefa ragar Man United minti hudu da wasa.

Kwallon ita ce ta uku da yake ci a jere da Liverpool ke samun nasara a wasanninta na Premier a bana.

Liverpool ce ta daya a tebur bayan wasanni uku da kwallaye uku da maki tara.

Sakamakon ya sa kociyan United David Moyes ya ci gaba da rashin nasara a gidan Liverpool, Anfield.

Kociyan ya yi fatan nasara a wannan karon da Man United bayan wasanni 12 a Anfield yana shan kashi amma ba ta samu ba.

Wayne Rooney bai buga wa Manchester ba saboda raunin da ya ji a lokacin atisaye a ka.

Hakan ya sa ba zai buga wa Ingila wasanninta na neman zuwa gasar Kofin Duniya ba da Moldova da Ukraine.

Karin bayani