Aston Villa ta sayi Kozak

libor kozak
Image caption ''zai taimaka gaya a kan abin da muke da shi'' in ji Lambert

Aston Villa ta sayi dan wasan Czech Libor Kozak daga Lazio a kan kusan fam miliyan 7.

Dan wasan wanda ya fi jefa kwallaye raga a gasar Europa da ta wuce ya kulla yarjejeniyar shekaru hudu ne.

Kozak mai shekaru 24 ya buga wa kasarsa wasa sau hudu kuma shi ne na takwas da Villa ta saya a bazaran nan.

Kociyan Villa Paul Lambert ya ce zuwansa zai rage nauyin da ake dora wa Christian Benteke.

Benteke ya ci wa klub din kwallaye 22 a wasannin Premier 37 tun da ya zo daga kungiyar Genk ta Belgium shekara daya da ta wuce.

Karin bayani