Man United ta sayi Fellaini

marouane fellaini
Image caption Fellaini yana da sauran shekara uku a Everton amma kungiyar ta sayar da shi

Manchester United ta sayi Marouane Fellaini daga Everton a kan fam miliyan 27.5

Fellaini dan Belgium mai shekaru 25 ya je Goodison ne daga Standard Liege a kan fam miliyan 15 a 2008 kuma kwantiraginsa da Everton har zuwa 2016 ne.

Tun a watan Agusta ne Man United ta nemi sayen Fellaini da Leighton Baines su biyu a kan fam miliyan 28.

Guillermo Varela shi ne dan wasa na biyu da Manchester United ta saya a wannan bazara.