Liverpool ta sayi Sakho da Ilori

sakho da ilori
Image caption Sakho shi ne dan wasa mafi tsada da Liverpool ta saya a bana

Liverpool ta sayi 'yan wasan baya Mamadou Sakho da Tiago Ilori a kan kusan fam miliyan 25.

Ana ganin cinikin Sakho mai shekaru 23 da ya yi wa Faransa wasa sau 14 daga PSG ya kai kusan fam miliyan 18.

Ilori mai shekaru 20 wanda ya bar Sporting Lisbon a kan fam miliyan 7 ya bugawa Portugal wasa a matakin matasa.

Amma kuma zai iya yi wa Ingila wasa saboda an haife shi a London.

Kawo yanzu Liverpool ta sayi 'yan wasa bakwai ke nan a kakar wasa ta bana.

Karin bayani