Moses ya koma Liverpool

Image caption Victor Moses

Liverpool ta sayi dan kwallon Chelsea Victor Moses a matsayin aro har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Dan shekaru 22, tsohon dan kwallon Crystal Palace da Wigan ya hade da Liverpool tare da sabbin 'yan kwallo Mamadou Sakho da Tiago Ilori.

Moses yace "manufar kulob din shine kasancewa cikin manyan kungiyoyi hudu na farko da kuma fafatawa a gasar zakarun Turai".

Moses ya zira kwallo daya cikin wasanni 23 a Chelsea tun lokacin daya koma kulob din daga Wigan a kan fan miliyon tara a watan Agustan bara.

Dan kwallon Najeriya din ya taimakawa Chelsea ta lashe gasar Europa inda ya zira kwallaye hudu.

Kafin komawarsa Liverpool, Moses bai bugawa Chelsea kwallo ba a karkashin sabon koci Jose Mourinho.

Karin bayani