Odemwingie ya tafi Cardiff

peter odemwingie
Image caption Odemwingie bai yi wa West Brom wasa ba a kakar wasannin nan

Cardiff City ta sayi Peter Odemwingie daga West Brom a kan fam miliyan 2.25 na tsawon shekara biyu.

Swansea City da Stoke City a da su ma sun so sayen dan Najeriyar mai shekaru 32.

Tun lokacin da Odemwingie ya yi kokarin tilasta barin QPR a watan Janairu su ka samu rashin jituwa ba a sa shi a wasa sosai.

Cardiff ta na da maki hudu a wasanni uku da ta yi na farko na Premier, ta fara da rashin nasara a gidan West Ham.

Sannan kuma ta ba wa Manchester City mamaki ta casa ta kafin ta yi canajaras da Everton.

Wasan kungiyar na gaba shi ne da Hull City ranar 14 ga watan Satumba.

Karin bayani