Cinikin Ozil ne mai tsoka a ranar karshe

Dan wasa Mesut Ozil
Image caption A ranar Litinin ne aka rufe saye da aron 'yan wasa na kakar wasannin bana

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta sayi Metsul Ozil kan kudi sama da fam miliyan 42, daga kulob din Real Madrid.

Cinikinsa ne dai mafi tsoka a ranar karshe na sayen 'yan wasan nahiyar Turai.

Ita kuwa Everton ta dauki James McCarthy daga Wigan kan kudi fam miliyon 13, ta kuma karbo 'yan wasa Gareth Barry daga Manchester City da Romelu Lukaku daga Chelsea aro.

An kashe akalla fam miliyon 140 a sayen 'yan wasa a Ingila a ranar karshe da aka rufe sayen 'yan wasan na nahiyar Turai.

Fam miliyon 630 aka kashe a sayan 'yan wasan a Ingila kadai, kuma kaso mafi tsoka shi ne cinikin Gareth Bale daga Tottenham zuwa Real Madrid kan kudi sama da fam miliyon 85.