Kofin Duniya: Wasannin Afrika

kofin duniya
Image caption Kasashe goma za a kasa a rukunai biyar da a karshe za a fitar da biyar daga ciki su wakilici Afrika

A karshen makon nan ne za a samu kasashe bakwai da za a hada da Algeria da Masar da Ivory Coast su zama goma da za a tankade biyar daga cikinsu da za su wakilci Afrika a gasar Kofin Duniya.

Su dai kasashen Algeria da Masar da Ivory Coast tuni suka samu gurbi a jerin 'yan goma da za a raba rukunai a tsakaninsu.

Wasannin da za a yi:

Ranar Juma'a

Ghana da Zambia

Wasu daga cikin na Asabar:

South Africa v Botswana :Nigeria v Malawi

Burkina Faso v Gabon: Niger v Congo

Ivory Coast v Morocco : Senegal v Uganda

Wasu daga cikin na ranar Lahadi

Cameroon v Libya: Togo v Congo DR

Karin bayani