Atsu na murnar komawa Chelsea

Image caption Dan Ghana Christian Atsu

Dan kwallon Ghana Christian Atsu ya nuna jin dadinsa game da kulla yarjejeniya da kulob din Chelsea.

Ya sanya hannu ne a yarjejeniyar shekaru biyar tare da Chelsea amma kuma take aka mika shi aro zuwa kulob din Vitesse Arnhem na Holland.

Dan wasan mai shekaru 21 zai iya buga gaba ta bangaren hagu ko kuma a matsayin dan wasa mai zira kwallo.

Yanzu haka Atsu yana Ghana inda tawagar Black Stars za ta kara da Zambia a Kumasi a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil.

Karin bayani