Man U na bukatar taimako — Comolli

david moyes
Image caption ''Lokacin da Moyes ya dawo Man United lokaci ya kure na zaben 'yan wasa'' in ji Comolli

Manchester United na bukatar mai taimaka mata wajen sayen 'yan wasa in ji tsohon darektan wasanni na Tottenham da Liverpool Damien Comolli.

Kociyan Manchester United David Moyes da babban jami'in kungiyar Ed Woodward sababbi ne a ayyukansu a kungiyar.

Hakan yasa suka gamu da matsala a lokacin kasuwar sayen 'yan wasan da a ka rufe ranar biyu ga watan Satumban nan.

Kungiyar ta kasa samun sayen da yawa daga cikin 'yan wasan da ta so in ban da Marouane Fellaini da ta saya a ranar karshe a kan fam miliyan 27.5.

A kan hakan Damien Comolli ya ce idan da akwai kungiyar da take bukatar darektan wasanni to Manchester United ce.

Karin bayani