Wawrinka ya yi waje da Murray

  • 5 Satumba 2013
stanislas wawrinka
''Ina ganin watakila yau ba ranata ba cei'' in ji Andy Murray

Andy Murray ya kasa kare kofinsa na gasar tennis ta Amurka a karawarsa da Stanislas Wawrinka.

Wawrinka ya yi wa je da shi a wasan gab da na kusa da karshe na gasar da maki 6-4 6-3 6-2.

Stanislas Wawrinka na tara a duniya dan Switzerland ya yi galaba a kan Murray na uku a duniya.

Wannan na daya daga manyan nasarorin da Wawrinka ya taba yi da ta sa Murray zai rasa kofinsa a ranar Litinin.

Karin bayani