Demichelis zai yi jinyar makwanni 6

Image caption Martin Demichelis

Sabon dan kwallon Manchester City, Martin Demichelis zai yi jinyar makwanni shida saboda rauni a idon sawunsa.

Dan wasan mai shekaru 32, a ranar Lahadi ya koma Atletico Madrid a kan fan miliyon hudu da dubu dari biyu.

Wannan raunin ya kara janyowa City matsala saboda a yanzu haka Vincent Kompany da kuma Micah Richards suna jinya.

Demichelis ya yi kwallo karkashin Manuel Pellegrini a Malaga da kuma River Plate.

A yanzu dai 'yan wasan baya guda biyu ne kawai lafiyayyu Manchester City ke dasu wato Matija Nastasic da kuma Joleon Lescott .

Karin bayani