Assad ya musanta kai harin guba

hirar Assad
Image caption Assad ya kalubalanci Obama ya nuna shedar gwamnatinsa ce ta kai harin makamai masu guba

Shugaban Syria Bashar al Asssad ya musanta cewa shi ke da alhakin harin makamai masu guba da aka kai Damascus a watan da ya wuce.

Assad ya bayyan hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Amurka CBS.

Shugaban ya ce Syria da kawayenta za su maida martanin duk wani hari da Amurka za ta kai kasarsa.

Wakilin BBC ya ce shugaban ya shirya hirar ne ta zo daidai da lokacin da 'yan majalisar Amurka ke mahawara a kan batun kai wa Syria harin.

Karin bayani