Nadal gwarzon dan wasa ne - Djokovic.

Nadal vs Djokovic
Image caption Nadal mai shekaru 27 ya sami nasara a wasanni 21 a filin tsandauri.

Ranar litinin dinnan za'a kara a wasan karshe na kwallon tenis ta Us Open, tsakanin Rafeal Nadal da Novak Djokovic.

Djokovic ya ce Nadal kwararren dan wasa ne, da ake ganin zai lashe gasar.

Ya kara da cewar dan wasan yana da hazaka da kokarin ganin anyi tata burza da shi a wasa.

Nadal mai shekaru 27, ya sami nasara a wasanni 21 da ya kara a turbaya, tun lokacin da ya dawo daga jinya a raunin da ya samu a gwiwarsa cikin wannan shekarar.