Zan iya komawa Manchester - Herrera

David Moyes
Image caption Herrera na tararabin ko Manchester United za ta iya sasantawa da Athletic Bilbao

Ander Herrera ya jaddadawa Manchester United cewa sai sun biya yarjejeniyar kwantiraginsa idan suna son ya bar Athletic Bilbao.

Herrera, mai shekaru 24, ya ce Manchester United za ta sake yunkurin sayensa a watan Janairu mai zuwa.

Ya ce zai iya barin Athletic Bilbao idan Manchester United za ta biya euro miliyan 36.

Haka kuma sai an rarrashi dan wasan kafin ya baro kasar Spain.

Karin bayani