Bach ya zama shugaban Olympic

Image caption Bach ya ce zai gudanar da mulki domin hada kan 'yan kwamatin Olympic

Kwamitin Gasar Olympic na duniya ya zabi Thomas Bach a matsayin sabon shugabansa.

Mista Bach lauya ne kuma shi ne mataimakin shugaban kwamitin gabanin zaben da aka yi masa.

Shugaban kwamitin mai barin gado Jacques Rogge ne ya bayar da sanarwar zaben Bach a matsayin shugaba na tara.

Mista Bach ne dan wasa na farko da ya lashe kyautar zinare wanda ya zama shugaban kwamatin Gasar Olympic.

Ya lashe kyautar ne a wasan jifa a shekarar 1976.

A jawabinsa na amincewa da zaben, sabon shugaban kwamitin Olympic din ya ce zai gudanar da mulkinsa ne domin tabbatar da hadin kai duk da irin bambance-bambancen da ke tsakanin mambobin kwamitin.

Wakilin BBC ya ce babban kalubalen da sabon shugaban zai fuskanta shi ne Gasar Olympic ta bazara da za a gudanar a Sochi, wacce ke cike da rudani; da kuma jinkirin da ake samu wanda ke yin tasiri a gasar da za a yi a Rio de Janeiro a shekarar 2016.

Karin bayani