'Bale zai fuskanci kalubale a Madrid'

Dan wasa Gareth Bale
Image caption Dan wasa Gareth Bale

Dan wasa Gareth Bale zai fuskanci kalubale, kasancewarsa dan wasan da ya fi tsada a duniya da kulob din Real Madrid ya saya, inji Zlatan Ibrahimavich.

Ibrahimavich mai shekaru 31, tsohon dan wasan Juventus da Barcelona, wanda yanzu yake wasa a PSG, yace sai Gareth ya zage dantse, ganin cewa za'a bukaci kyakkawan sakamako a wasansa.

Real Madrid ta sayo Gareth Bale daga Tottenham kan kudi kimanin euro miliyan 100.

Kuma ana sa ran dan wasan zai fara takawa Real Madrid leda, a ranar Asabar a wasansu da Villareal.