Shevchenko zai buga gasar golf

Image caption Andriy Shevchenko

Tsohon dan wasan Chelsea, Andriy Shevchenko zai fara gasar wasan golf na cin kofin 'Challenge Tour' a ranar Alhamis, cikin wasan zakaru da birnin Kharkov dake Ukraine zai karbi bakunci.

Shevchenko mai shekaru 36, ya yi ritayar wasan kwallon kafa, bayan gasar cin kofin nahiyar Turai a shekara ta 2012, tun a lokacin ya tsunduma wasan golf.

Dan wasan yace wannan itace gasa mai girma da zai fara bugawa.

Shevchenko da a baya ya bugawa AC Milan da Dynamo Kiev wasa, zai fafata da kwararrun yan wasa da suka hada da tsohon zakaran kofin Ryder Oliver Wilson da zakaran kofin nahiyar turai karo uku Nick Dougherty .

Shima tsohon lamba daya a wasan kwallon tennis Yevgeny Kafelnikov, mai shekaru 39, zai fafata a wasan.