Ireland ta raba gari da Trapattoni

Image caption Giovanni Trapattoni

Kocin Jamhuriyar Ireland, Giovanni Trapattoni ya ajiye aiki don radin kansa, sakamakon rashin nasara daya samu lokacin da suka kara a wasan neman shiga gasar kofin duniya tsakaninsu da kasar Austria.

Hukumar wasan kwallon kafa ta kasar ce dai ta bada sanarwar ajiye aikin nasa a ranar Laraba, bayan da ta zauna taro tare da mataimakin sa Marco Tardelli.

Tun farko yarjejeniyarsa za ta kare da kasar ne a watan Mayu na shekarar 2014.

A tsawon shekaru biyar da ya horadda kasar, ya tsallakar da kasar zuwa gasar wasan cin kofin nahiyar Turai ta shekarar 2012.