Ameobi na murnar cin kwallo

Image caption Shola Ameobi

Dan kwallon Najeriya, Shola Ameobi ya ce ya yi murna sosai saboda kwallon da ya zira na farko sanye da rigar kwallon Najeriya, a wasan da suka doke Burkina Faso daci hudu da daya.

Dan wasan Newscastle din yace " daga karshe dai na zira kwallo, ina murna".

Ameobi wanda ya bugawa Ingila kwallo a matakin 'yan kasada shekaru 21, a watan Nuwamba ne ya bugawa Super Eagles wasansa na farko bayanda FIFA ta amince ya bugawa kasarsa ta haihuwa.

Sakamakon sauran wasannin sada zumuncin da aka buga a Afrika:

Afrika ta Kudu 1-2 Zimbabwe

Nigeria 4-1 Burkina Faso

Canada 0-1 Mauritania

Japan 3-1 Ghana

Karin bayani