Farashin tikitin wasan kwallo ya ragu

Gasar wasan premier
Image caption Gasar wasan premier

Matsakaicin farashin tikitin wasan kwallo, na manyan kulob-kulob hudu na saman teburin gasar premier ta Ingila ya fadi.

Wani nazari da sashen wasanni na BBC ya gudanar ya nuna cewa, farashin ya fadi da sama da kashi biyu cikin dari a shekarar 2013 zuwa 2014.

Ministan wasanni na Birtaniya, Hugh Robertson ya ce "Wannan labari ne mai dadi ga masoya wasan kwallo, amma ya zo ne bayan kwashe shekaru ana samun kari a farashin."

Farashin tikiti mafi araha na kallon wasannin kulob-kulob hudu na gasar premier na mutum babba, ya ragu daga fam 344.63 a shekarar 2012 zuwa fam 336.23 a 2013.