Farashin tikitin kwallo ya fadi a Ingila

Image caption Dubban mutane ne ke shiga kallon kwallon a Ingila

Farashin tikitin shiga kallon kwallo a Ingila ya fadi da kashi 2.4 cikin 100, kamar yadda binciken BBC ya nuna.

Binciken ya nuna cewar farashin tikitin matakai hudu ya ragu a kakar wasa ta 2013-14.

Binciken na shekara ya shafin manyan kungiyoyi 166 dake taka leda a matakai goma na gasar kwallon kafa a Birtaniya.

An gudanar da bincikenne a gasar kwallo biyar a Ingila, hudu a Scotland da kuma gasar kwallon mata.

Binciken da aka gudanar a bara ya nuna cewar farashin tikitin kwallo a Ingila ya tashi da kashi 11 cikin 100.

Karin bayani